Isa ga babban shafi
Faransa-Afrika

Shugaban Faransa zai gana da shugabanin Cote D'Ivoire da Senegal a Paris

Shugaban Faransa Emmanuel Macron zai gana da shugaban Cote D’Ivoire Alassane Ouatarra a gobe lahadi a fadar sa dake birni Paris, bayan haka Macron zai haduwa da shugaban Sanegal Macky Sall ranar litinin .

Emmanuel Macron Shugaban kasar Faransa
Emmanuel Macron Shugaban kasar Faransa REUTERS/Charles Platiau
Talla

Shughabanin za su yi bitar wasu daga cikin muhiman batutuwa da suka shafi halakar Faransa da kasashen da ta rena , diflomasiya tsakaninta da su.

Shugaba Ouattara na kasar Cote D’ivoire ne shugaban Afrika na farko da Shugaban Faransa Emmanuel Macron zai ganawa da shi tun bayan kama rantsuwa soma aiki ranar 14 ga watan mayu shekarar nan da muke ciki.

Ya zuwa yanzu Shugaban Faransa Emmanuel Macron bai bayyana wata siyasa ta musaman da yake da ita zuwa kasashen Afrika.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.