rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Najeriya Muhammadu Buhari

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Yaushe Buhari zai dawo Najeriya ?

media
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari venturesafrica

Likitoci da ke diba lafiyar shugaban Najeriya Muhammadu Buhari sun ce a yau za su gudanar da gwaje gwaje akansa, inda sakamakon gwajin ne zai tantance lokacin da shugaban zai dawo.


Kamfanin dillacin labaran Reuters ya ambato wata majiya daga fadar shugaban Najeriya tana cewa Buhari ya fasa dawo wa a karshen mako, sabanin yadda aka yi hasashen zai dawo a ranar Lahadi.

Majiyar ta ce shugaba Buhari ba zai dawo gida ba domin akwai wasu gwaje-gwaje da likitoci za su yi ma sa a yau Litinin.

Ko Yaushe Buhari zai dawo ? wannan ita ce tambayar da ke bakin ‘yan Najeriya.

A watan jiya ne shugaba Buhari ya tafi London domin sake diba lafiyarsa, bayan shafe watanni biyu ba ya Najeriya a tafiyarsa ta watan Janairu.

Har yanzu dai ‘yan Najeriya ba su san irin rashin lafiyar da ke damun shugabansu ba.