Isa ga babban shafi
Kenya

Gini mai hawa bakwai ya rubta da mutane a Kenya

Mutane da dama sun bace bayan rubtawar wani bene mai hawa bakwai a cikin daren da ya gabata a Nairobi, babban birnin Kenya kamar masu aikin ceto suka bayyana.

Gini mai hawa bakwai da ya rushe a Nairobi na Kenya
Gini mai hawa bakwai da ya rushe a Nairobi na Kenya REUTERS
Talla

Jami’an ‘yan sandan kasar sun ce, an kwashe kimanin mazauna ginin 121 a lokacin da ginin ya fara tsagewa kafin ya ruguzo daga bisani.

Mataimakin shugaban sashen hulda da jama’a a hukumar kiyaye hadura ta Kenya, Pius Masai ya ce, ana ci gaba da neman mutanen da rubtawar ta cika da su.

Masai ya ce, an yi amanna cewa, ginin ya danne wasu daga cikin mutanen da ake nema.

Mr. Masai ya bukaci dukkanin jama’a da su bada gudun mawa ta hanyar taimaka wa jami’an agajin gaggawa don ceto mutanen.

Ana dai yawan samun matsalar rushewar gidaje a Kenya, abin da ake dangantawa da cin hanci da rashawa da ke hana samar da kwakkwaran gini.

Ko a shekarar 2016, sai da mutane 49 suka mutu sakamakon wani gini mai hawa shida da ya rushe a arewa maso gabashin Kenya bayan an tafka ruwa kamar da bakin kwarya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.