Isa ga babban shafi
Najeriya

Kotu ta wanke Bukola Saraki

Kotun da’ar Ma’aikata a Najeriya, ta wanke shugaban Majalisar Dattijan Kasar, Bukola Saraki, daga shari’ar zarge-zargen da ake masa na kin bayyana gaskiyar kadarorinsa a lokacin da ya ke Gwamnan Kwara.

Shugaban Majalisar dattijan Najeriya Bukola Saraki tare da mataimakinsa Ekweremadu suna murna bayan janye karar zarginsu da sauya doka
Shugaban Majalisar dattijan Najeriya Bukola Saraki tare da mataimakinsa Ekweremadu suna murna bayan janye karar zarginsu da sauya doka punch
Talla

Gwamnatin Tarayyar ce ta gurfanar da Saraki a gaban kotun da ake tuhuma kan laifufuka 13, a Satumba 2015 bayan Lashe kujeran shugabancin Majalisar.

Daga cikin laifukan da ake zargin Saraki, har da zargin karbar albashi biyu daga 2003 zuwa 2011 a lokacin da yana Sanata bayan ya sauka daga mukamin gwamna.

Saraki dai ya musanta dukkanin zarge-zargen.

Daya daga cikin lauyoyin da ke kare shugaban Majalisar Dattijan, Mahmoud Magaji ya shaidawa RFI Hausa cewa hujjojin da masu gabatar da kara suka gabatar bas u da wani karfin da za su tabbatar da zargin da ake wa Saraki.

Yanzu dai masu zargin Saraki na iya daukaka kara bayan wanke shi da kotun da’ar ma’aikata ta yi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.