rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Libya ICC

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Kotun ICC ta bukaci a gaggauta cafke Seif al-Islam Ghaddafi

media
Kotun ICC na tuhumar Saïf al-Islam Ghaddafi da aikata laifukan yaki MAHMUD TURKIA / AFP

Babbar mai gabatar da kara a Kotun duniya ta ICC da ke hukunta manyan laifuka Fatou Bensouda ta bukaci a gaggauta cafke Seif al-Islam dan marigayi Kanal Ghaddafi bayan sakinsa a Libya.


Seif Islam Ghaddafi ya samu afuwa ne daga wata kungiyar ‘yan tawaye da ke iko da yankin Zintan a yammacin Libya.

Babbar mai shigar da kara ta Kotun Duniyar Fatou Bensouda, ta ce ba ruwan kotun da wani shirin afuwa, saboda haka tana fatan za a cafke dan tsohon shugaban Libya Kanal Ghaddafi kamar yadda sammacin shekara ta 2011 ya bukata.

Islam ya shafe shekaru 5 a tsare, kuma ya samu afuwa ne karkashin wata doka da majalisar gwamnatin gabashin Libya ta amince a watan Ramadan.

Yanzu dai ba a san inda Seif Islam ya ke ba tun bayan sakinsa a ranar Juma'a.