Yau Ntaganda zai kare kansa a kotun ICC
Yau tsohon kwamnadan 'yan tawayen Congo, Bosco Ntaganda zai fara jawabi a gaban kotun hukunta manyan laifufuka ta duniya don kare kansa daga zargin aikata lafufukan yaki.
Wallafawa ranar:
Ana tuhumar Ntaganda da laifin kisa da fyade ga faraen hula da kuma sace dukiyarsu a lokacin da dakarunsa suka kutsa lardin Ituri da ke Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya tsakanin shekarar 2002 zuwa 2003.
Lauyansa Stephane Bourgon ya ce, Ntanganda zai bayyana duk abin da ya faru a wancan lokacin.
Akalla mutane 60,000 aka kashe a tashin hankalin da aka samu a Ituri daga shekarar 1999 kamar yadda kungiyoyin kare hakkin bil adama suka bayyana.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu