Isa ga babban shafi
Najeriya

Amnesty ta jaddada matsayinta kan sojin Najeriya

Wani Kwamiti na musamman da rundunar Sojin Najeriya ta kafa ya wanke sojojin kasar da ake zargi da cin zarafin bil’adama a yankin arewa maso gabashi da kuma kudu maso gabashin kasar.

Sojojin Najeriya da ke yaki da Boko Haram
Sojojin Najeriya da ke yaki da Boko Haram © Getty Images
Talla

Rundunar sojin Najeriya ta ce babu hujjoji da suka tabbatar da zargin da ake wa kwamandojinta.

Kungiyar kare hakkin bil’adama ta Amnesty International ta fitar da rahoto mai shafi 133 a watan Yunin 2015 da ke zargin sojojin Najeriya da kashe mutane da sunan  Boko Haram da kuma kashe masu fafatukar kafa kasar Biafra.

Amnesty ta zargi sojin da cin zarafin bil’adama tare da amfani da karfin da ya wuce kima kan jama’a.

Har yanzu Amnesty ta ce, tana nan kan bakarta kamar yadda jami’inta a Najeriya Isa Sunusi ya shaidawa RFI Hausa.

Sanusi ya ce rahoton na Sojin Najeriya ya nuna kamar mai laifi ne ya wanke kansa.

Rahoton Amnesty ya zayyana sojoji 6 da ta bukaci a hukunta kan aikata laifuka da suka shafi kisa da azabtar da mutane da sunan yaki da Boko Haram.

Rahoton Amnesty ya yi zargin cewa sama da mutane 1,200 Sojoji suka kashe, tare da cafke dubban mutane yadda suka ga dama.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.