Masar-Saudiya
Majalisar Masar ta amince a mikawa Saudiya Tsibirai biyu
Majalisar dokokin Masar ta amince da shirin mikawa kasar Saudi Arabia wasu tsibirai guda biyu da ake takaddama akai.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Talla
Shirin mika wadannan tsibirai guda biyu ya haifar da zanga zanga a Masar, yayin da wasu suka shigar da kara a gaban kotu domin kalubalantar matakin.
Ranar talata wasu 'Yan Jaridu a Masar sun gudanar da zanga zangar adawa da mika tsibiran kafin 'Yan sanda su tarwatsa su.
Ana zargin shugaba Abdel Fatah al Sisi da mikan tsibiran domin samun wasu bukatu daga Saudiyan.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu