Isa ga babban shafi
Jamhuriyar Benin

Motar safa ta yi karo da jirgin kasa a Benin

Rahotanni daga Jamhuriyar Benin sun ce mutane da dama sun mutu lokacin da wata motar safa mai gudun wuce kima ta yi karo da jirgin kasa.

Mutane da dama sun mutu bayan motar safa mai gudun wuce kima ta yi karo da jirgin kasa a Benin
Mutane da dama sun mutu bayan motar safa mai gudun wuce kima ta yi karo da jirgin kasa a Benin RFI/Delphine Bousquet
Talla

Wani jami’in kamfanin jiragen kasa, Ramani Kassomou, ya ce jirgin na tafiya ne akan hanyar Cotonou zuwa Parakou lokacin da hadarin ya auku.

Ministan cikin gida Sacca Lafia ya tababtar da mutuwar mutane da dama ba tare da bada adadi ba.

Kamfanin Bollore na Faransa ke tafiyar da jiragen kasa wanda ke dauke da jarin Gwamnatocin Benin da Nijar.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.