rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Qatar Diflomasiya Djibouti Eritrea

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Qatar ta janye dakarunta a kasar Djibouti da Eritrea

media
Ministan harkokin wajen Qatar Mohammed bin Abdulrahman al-Thani REUTERS/Maxim Shemetov

Qatar ta sanar da janye dakarun ta da ke aikin samar da zaman lafiya akan iyakar kasar Djibouti da Eritrea.


Ma’aikatar harkokin wajen kasar ta sanar da daukar matakin ba tare da bayyana dalilan janye sojojin ba.

Sanarwar ta ce Qatar zata ci gaba da zama ‘yar ba ruwan mu wajen sasanta rikicin da ke tsakanin ‘yan uwa da kuma kawayen ta.

Sai dai wasu bayanai sun ce matakin ya zo ne sakamakon goyan bayan Saudi Arabia da Djibouti ta yi a rikicin da suke yi yanzu haka.