rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Najeriya APC

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

APC ta kori Abdulmumin Jibrin daga cikinta

media
Dan Majalisar Wakilan Najeriya Abdulmumin Jibrin

A Najeriya, jam’iyyar APC ta sanar da korar dan majalisar wakilan tarayyar kasar Abdulmumin Jibrin daga cikinta baki daya bayan samun sa da laifin yi wa jam’iyyar zagon kasa.


Shugaban jam’iyyar reshen karamar hukumar mulkin Bebeji wadda ita ce mazabar Jibrin a jihar Kano Sani Ranka, ya ce kafin daukar matakin sai da suka kafa wani kwamiti mai mutane biyar wanda ya gudanar da bincike tare da kokarin ganawa da dan majalisar amma kuma ya ki.

Abdulmumin Jibrin ya fara samun matsala da jam’iyyarsa ta APC ne a bara, bayan da ya fito ya yi zargin cewa an yi cushe a cikin kasafin kudin kasar na shekarar da ta gabata, zargin da ya sa aka dakatar da shi aikin dan majalisa na tsawon watanni.