rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Najeriya

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Lagos, Kaduna da Kano za su amfana da asusun musamman na man fetur

media
Gidan man NNPC a Najeriya REUTERS/Stringer

Sabuwar doka game da bincike, hakowa da kuma cinikin man fetur a Najeriya PIB, ta bukaci a sanya jihohin Kano, Kaduna da Legas a cikin wadanda za su ci moriyar kaso na musamman da ake bai wa jihohin da suka mallaki man fetur kawai.


Dokar, wadda yanzu haka majalisar wakilai ke kan yi ma ta bita, ta yi tanade-tanade ga jihohin da ke da matatun mai, defo-defo na mai ko kuma wadanda bututun mai ya ratsa a cikinsu.

Legas da Kano na matsayin jihohin da ke kunshe da manyan defo-defo na mai a kasar, sai Kaduna inda ake da matatar mai, dalilan da suka sa dokar ke neman a kebe wa jihohin wasu kudade kamar yadda ake yi wa jihohin da ake hako mai a cikinsu.