rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Nijar

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Mutane 11 ne suka mutu a ambaliyar ruwan birnin Yamai

media
Ambaliyar ruwa a Yamai, Nijar

Mahukuntan Jamhuriyar Nijar sun tabbatar da mutuwar mutane 11 sakamakon ruwan sama mai karfi da ya sauka a tsawon kwanaki biyu a birinin Yamai fadar gwamnatin kasar.


Mafi yawa daga cikin wadanda suka rasa rayukansu kananan yara ne da kuma wadanda gidaje suka fadi a kansu.

Ambaliyar ta bana ta zo wa kasar da ba zata, lura da cewa duka duka bai wuce wata daya da daminar bana ta fara sauka ba.

A daminar bara ma an samu asarar rayukan mutane sama da 50 sakamakon ambaliyar ruwan wadda ta shafi mutane sama da dubu dari tare da kashe dabbobi sama da dubu 20 a sassan kasar.