rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Djibouti Eritrea

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Kungiyar Tarayyar Africa Ta Ja Kunnin Kasashen Djibouti da Eritrea

media
Shugabannin Kasashen Kungiyar Tarayyar Africa bayan wani taro a cibiyar Kungiyar dake Habasha AFP/Zacharias ABUBEKER

Kungiyar Tarayyar Africa ta roki kasashen Djibouti da Eritria da su rungumi tattaunawan zaman lafiya maimakon kai ruwa rana a rikin da ya sarke tsakaninsu saboda batun kan iyaka.


A jiya Juma’a  Ministan waje na kasar Djibouti Mahamoud Ali Youssouf ke zargin Eritria da cewa ta mamaye tsaunukan Dumeira inda suke takaddamar sa.

A baya an jibge sojan wanzar da zaman lafiya na kasar Qatar  a kan iyakan kasashen biyu, amma kuma tun da sojan suka janye ne aka fara samun sabuwar takaddamar.

A sanarwar da Kungiyar Tarayyar Turai ta fitar yau Asabar, da sa hannun Moussa Faki Mahamat na cewa kasashen biyu su kiyaye da ga tada husuma.