rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Mali Nijar Burkina Faso

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

'Yan tawayen Mali sun sake kaiwa sojojin kasar hari

media
Tsaro a yankin arewacin Mali daga rundunar Barkhane REUTERS/Christophe Petit Tesson/Pool

A kasar Mali mutane uku da suka hada da wani soji ne suka rasa rayukan su bayan da wasu yan bindiga da ake zaton yan tawayen arewacin kasar ne suka kai masu hari a wasu shigayen bicinke dake kan iyakokin Nijar, Burkina Faso da kasar ta Mali.


Rahotani daga wani kauye mai suna Soumouni na nuni cewa an hango wasu mutane dauke da mugan makamai a kan babura inda suka habkawa wasu manoma tareda kashe biyu daga cikin su.

Duk da kokarin hukumomin kasar na shawo kan matsallolin tsaro akwai wasu yankunan kasar da yan bidinga ke ci gaba tada zaune tsaye.
Yankin Asongo ranar alhamis da ta gabata wata motar soji ta taka nakiya, inda aka samu mutuwar soji daya wasu biyu can daban suka samu rauni.