rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya Tarayyar Afrika

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Gwamnati da 'Yan Tawaye a Janhuriyar Tsakiyar Afrika Sun Amince da Sulhu

media
Sojan wanzar da zaman lafiya na kasashen Africa dake aiki a Bangui EUTERS/Luc Gnago

Yau ne Gwamnatin kasar Janhuriyar Tsakiyar Afrika da bangaren ‘yan tawayen kasar suka sanya hannu cikin yarjejeniyar tsagaita wuta a wani taron da aka yi a Rome da niyyar kawo karshen tarzoma a fadin kasar.

 


Ana sa ran bayan sulhun kungiyoyin dake dauke da makamai za su shiga Gwamnati domin ganin sun daina tada zaune tsaye.

Kasar Janhuriyar Tsakiyar Afrika wadda ake ganin a duniya ita ce mafi koma baya ta fannin komi, na fama da tashe-tashen hankula  musamman na addini tun shekara ta 2013.

Rayukan mutane sama da 100 suka mutu yayinda wasu dubu dari suka tsere daga gidajen su.