rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Mali Ta'addanci

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

‘Yan bindiga sun kai hari inda turawa ke shakatawa a Mali

media
Wurin shakatawar Le Campement Kangaba inda 'yan bindiga suka kai hari a Mali REUTERS/ REUTERS TV

An kashe ‘yan bidiga hudu wadanda suka yi yunkurin yin garkuwa da jama’a a wani wuri da masu yawon bude ido ke shakatawa kusa da birnin Bamako a kasar Mali.


‘Yan bindigar sun isa ne saman babur inda suka abkawa wajen shakatawar da yawanci Turawa ke halarta a karshen mako.

Ministan tsaron cikin gidan kasar Salif Traore ya ce da farko maharan sun yi garkuwa da mutane 36 cikin har da ‘yan asalin kasashen ketare kafin daga bisani jami’an tsaro su ceto su.

Biyu daga cikin wadanda aka yi garkuwa da su sun rasa rayukansu a cewar ministan.

Traore ya shaidawa RFI cewa an kashe biyar daga cikin maharan, kuma an cafke wani mutum daya da ake zaton cewa yana da alaka da ‘yan bindigar.

Ga alama an kai harin ne da nufin hallaka ‘yan kasashen waje, domin a lokacin harin akwai Faransawa 14, ‘yan Mali 13, dan Kamaru daya da kuma dan Italiya daya da ‘yan Spain biyu, da ‘yan Holland biyu, da dan kasar Masar guda sai kuma wasu ‘yan Kenya biyu.