rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Najeriya Tattalin Arziki

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

‘Yan canji a Najeriya na son a samar da farashin bai-daya

media
Naira ta fara farfadowa akan dalar Amurka REUTERS/Joe Penney/Files

Kungiyar masu canjin kudi a Najeriya ta bukaci babban Bankin kasar da ya samar da farashin bai-daya na kudaden waje, wanda zai taimaka wajen karkato da hankulan masu zuba hannayen jari a kasar.


Najeriya da ke kan gaba wajen karfin tattalin arziki a Afrika na fama da matsalar farashin kudaden waje, inda farashin Mahajjata zuwa Saudiya ya banbata da na masu yawon shakatawa ko kuma biyan kudin makaranta a waje, yayin da farashin sari ga masu lasisi ya banbata da na kasuwannin bayen fage.

Kungiyar ‘yan canji ta ce, magance matsalar banbancin farashin na kudaden waje zai dawo da darajar Naira, abin da zai yi tasiri ga tattalin arzikin kasar.

Sakataren Kungiyar Alhaji Tanimu Ibrahim ya ce rarrabuwar farashin kudaden zai yi tasiri ga farashin kayayyaki.

A cewarsa, farashin bai-daya tare da kara yawan dala a kasuwa zai taimaka wajen farfado da darajar Naira.

Masharhanta dai na ganin daukar matakin tantance darajar Naira na da tasiri sosai ga masu saka jari musamman daga kasashen waje domin dajarar Naira zai ba su kwarin guiwar shigowa kasar.