rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Najeriya

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Za a yi mako biyu ana gyaran gadar Jirgin kasa daga Mokwa zuwa Jebba

media
Karyewar gada tsakanin Mokwa zuwa Jebba ya dakatar da zirga-zirga tsakanin arewaci da kudanci a Najeriya instablog9ja

Hukumar sufurin jiragen kasa a Najeriya ta ce za a dauki tsawon mako biyu kafin a gyara babbar gadar da ta hada garin Mokwa da Jebba sakamakon ruwan sama da ya lalata gadar jirgin kasa da ta mota a babbar hanyar da ta hada yankin arewacin Najeriya da kudanci a jihar Neja.


Jami’in hulda da jama’a na hukumar sufurin jiragen kasa a Najeriya, Yakubu Mahmud ya shaidawa RFI Hausa cewa ruwan sama mai karfi da aka yi ya karya gadar titin jirgin kasa da hanyar mota tsakanin Mokwa zuwa Jebba.

Karyewar gadar ya haifar da tsaiku na sufurin jiragen kasa daga Lagos zuwa Kano da motoci da ke jigila daga kudu zuwa arewacin Najeriya.

Rahotanni sun ce motocin da suka fito daga Lagos a kudancin Najeriya ba su iya wuce garin Jebba cikin jihar Kwara, yayin da wadanda suka fito daga yankin arewaci ba su iya wuce garin Mokwa a jihar Neja.

Mista Mahmud ya ce aikin gyaran gadar jirgin kasa zai dauki tsawon mako biyu domin injiniyoyi suna can suna aiki dare da rana.

Karyewar gadar na zuwa a yayin da ake dab da gudanar da bikin Sallah a Najeriya.