Sahel: Amurka da Faransa sun amince da kafa runduna ta musamman
Amurka da Faransa sun amince da daftarin da zai bukaci kafa runduna ta musamman, da zata kunshi sojoji 5,000 daga kasashe biyar na yankin Sahel, domin murkushe hare-haren ta’addancin da ke karuwa a yankin.
Wallafawa ranar:
Tun a watan Maris kasashe 5 na yankin Sahel, da suka hada da Burkina Faso, Chadi, Mali, Mauritania da Nijar, suka cimma jituwa kan kafa rundunar, a wani taro da suka yi a birnin Bamako, to sai dai ana bukatar amincewar MDD kafin ta fara aiki.
Wani lokaci a yau ake sa ran kwamitin tsaro na majalisar dinkin duniya zai kada kuri’ar amincewa da fara aikin rundunar.
A farkon watan da muke ciki, kungiyar tarayyar turai EU ta amince ta bayar da tallafin Euro miliyan 50 ga kasashen yankin Sahel din na G5 domin tafiyar da ayyukan rundunar, bayan da suka bukaci tallafin.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu