Boko Haram ta kashe mutane 6 a Kamaru
Akalla mutane takwas suka mutu a wasu hare haren kunar bakin wake da aka kai a garin Kolofata yankin arewa mai nisa a Kamaru kusa da iyaka Najeriya. Cikin wadanda suka mutu har da maharan guda biyu da fararen hula shida.
Wallafawa ranar:
An kai harin ne da marece a daidai lokacin da jama’a ke hada-hadar kasuwanci a Kolafata da ya saba fuskantar hare-hare daga ‘yan Boko Haram.
A farko watan Yunin bana an kai harin kunar bakin wake a yankin da ya kashe mutane 9, yayin da kuma aka kai wani hari a Limani kusa da Kolafata da ya kashe fararen hula biyu.
Kamaru da ke makwabtaka da Najeriya na cikin rundunar hadin guiwa da ke yaki da Boko Haram da suka addabi Yankin Arewa mai nisa.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu