Isa ga babban shafi
Ghana

Kotun Ghana ta bukaci a mayar da fursunonin Guantanamo zuwa Amurka

Kotun Kolin kasar Ghana ta bayyana dauko wasu fursunoni biyu daga Guantanamo zuwa kasar ba tare da amincewar Majalisar dokoki ba a matsayin abinda ya saba wa kundin tsarin mulkin kasar.

Fursunonin gidan yarin Guantanamo
Fursunonin gidan yarin Guantanamo REUTERS
Talla

A watan Janairun 2016 ne gwamnatin Ghana da kuma Amurka suka kulla yarjejeniyar ci gaba da kula fursunonin a cikin Ghana, matakin da alkalin kotun Sophia Akuffo ta ce ya kauce wa dokokin kasar.

Wasu ‘yan kasar Ghana ne suka shigar da kara a kotu domin kalubalantar amincewa da fursunonin na Guantanamo a cikin kasar inda suka ce shugaba John Mahama ya saba doka.

Alkalin kotun kolin Ghana ya bukaci a mayar da fursunonin zuwa Amurka, idan har majalisa ba ta amince da bukatar ba cikin watanni uku.

‘Yan asalin kasar Yemen ne guda biyu da ake zargi da alaka da ayyukan ta’addanci kasar Ghana ta karba daga hannun Amurka bayan sun shafe shekaru 10 a gidan yarin Guantanamo.

Rarraba fursunonin zuwa wasu kasashe na daga cikin manufofin tsohon shugaban Amurka Barack Obama kan alkawalin da ya dauka na rufe gidan yarin na Guantanamo da ake tsare wadanda ake zargi da laifukan ta’addanci.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.