rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Zimbabwe Mozambique Dabbobi

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Zimbabwe ta fara kwashe dabbobin daji zuwa Mozambique

media
Za a kwashe Namun dajin ne daga gandun dajin Sango Ranch zuwa gandun Zinave Mozambique http://www.ictsd.org

An fara gudanar da wani gagarumin aikin kwashe dubban dabbobin daji daga kasar Zimbabwe zuwa makociyarta Mozambique, a karkashin wani shiri na raya gandayen dajin Mozambique da suka zama wayam sakamakon yakin basasar shekaru 15 da kasar ta yi fama da shi.


Hukumar kare gandayen dajin Zimbabwe ta ce Giwaye 50 da Rakuman daji 100 da Jakunan dawa 200 da kuma Baka 200, na daga cikin dabbobi dubu bakwai da za a kora cikin wata tafiyar mai tsawon kilomita 600.

Dabbobin za su yi tafiya mai nisa da yawansu yak ai sama da 6,000. Wannan shi ne adadi mafi girma da aka canza wa dabbobin daji muhalli daga wata kasa zuwa wata kasa.

Za a shafe shekaru uku a karkashin shirin kafin sake rarraba namun dajin zuwa Zimbabwe da Afrika ta kudu.