Isa ga babban shafi
Congo-Brazzaville

Bincike kan ‘yar da kuma surukin shugaban kasar Congo-Brazzaville a Faransa

Kotu a Faransa na tuhumar ‘yar da kuma surukin shugaban kasar Congo-Brazzaville Denis Sassou-Nguesso da mallakar kadarori ciki har da gidaje wanda ake iya fassarawa a matsayin laifin halasta kudaden haram.

Sassou Nguesso Shugaban kasar Congo Brazzaville
Sassou Nguesso Shugaban kasar Congo Brazzaville STRINGER / AFP
Talla

Shekaru 7 bangaren shari’a ya share yana gudanar da bincike dangane da wannan batu, inda a cikin watan maris da ya gabata suka ambaci sunan Wilfrid Nguesso, yayin da a wannan karo aka bayyana Julienne Sassou-Nguesso da mijinta Guy Johson da hannu wajen halasta kudaden na haram

Daga cikin shugabannin kasashen Afirka da ake bincike ko kuma iyalansu, akwai marigayi Omar Bongo na Gabon, Denis Sassou-Nguesso na Congo-Brazzaville da kuma Toedoro Obiang Nguema na Equatorial Guinea.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.