rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Wasanni Tseren Gudu

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Har yanzu ban tsaida lokacin ritaya daga tseren gudu ba - Bolt

media
Zakaran tseren gudun mita 100 da na 200 na duniya dan kasar Jamaica, Usain Bolt yayin zantawa da manema labarai a birnin Ostrava na Jamhuriyar Czech. REUTERS/David W Cerny

Zakaran tseren gudu har sau takwas a wasannin Olympics, Ussain Bolt, ya ce mai yiwuwa ne, ya cigaba da haskawa a fagen nasa, bayan kammalla gasar tseren gudu ta duniya da za’a yi cikin watan Agusta mai zuwa a birnin London.


A baya Bolt mai shekaru 30, ya ce gasar tesren gudun da za’ayi a London, ita ce zata ta karshe da zai fafata, daga nan kuma a barwa ‘yan baya.

Sai dai yace bayan da ya tattauna da mai horar da shi, Glen Mills, a yanzu yana duba shawarar tsawaita cigaba da fafatawa a fagen na tseren gudu zuwa kakar wasa ta gaba.

Bolt zai fafata ne a gasar tseren gudun mita 200 a gasar duniya da za’a yi a London.

Har yanzu dai yana rike da kambun wasannin tseren gudun mita 100 da mita 200 wadanda ya lashe su tun a shekarar 2008, a birnin Biejing na kasar China.