Isa ga babban shafi
Sahel

Macron zai halarci taron kasashen Sahel

Shugaba Emmanuel Macron na Faransa zai halarci taron taron shugabannin kasashen yankin sahel 5 da zai tattauna batun fada da ayyukan ta’adanci a birnin Bamako na kasar Mali a ranar lahadi mai zuwa.

Dakarun Faransa da ke aikin tabbatar da tsaro a Mali
Dakarun Faransa da ke aikin tabbatar da tsaro a Mali AFP/Stephane de Sakutin
Talla

Taron wanda zai kasance na farko tun bayan da Majalisar Dinkin Duniya ta amince kasashen biyar Burkina Faso da Chadi da Mali da Mauritania da Nijar su kafa rundunar soji mai dakaru dubu biyar, zai tattauna hanyoyin da za a bi domin samar da kudaden da za a daukin nauyin tafiyar da wannan runduna ce.

Kasashen sun amince su kafa runduna ta musamman duk da cewa akwai dakarun wanzar da zaman lafiya na Majalisar dinkin Duniya 12,000 da dakarun Barkhane na Faransa 4,000 da ke aikin samar da tsaro a Mali.

Shugaba Macron zai yi kokarin ganin an samar wa rundunar da karin tallafi musamman daga kasashen Amurka da Jamus da Holland baya ga alkawalin yuro miliyan 50 da Tarayyar Turai ta ce za ta bayar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.