rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Nijar Mahamadou Issoufou

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

‘Yan jaridar Nijar sun shiga takun-saka da gwamnati

media
Shugaban Nijar Mahamadou Issoufou AFP / BOUREIMA HAMA

Kungiyoyin ‘yan jaridu sama da 20 suka fitar sanarwa da ke nuna damuwarsu dangane da yadda gwamnatin Jamhuriyar Nijar ke ci gaba da yin tsangwama wa ‘yan jarida, bayan da alkali ya bayar da umurnin ci gaba da tsare shugaban Jaridar Le Courrier Ali Soumana a gidan yari.


An zargi Soumana ne da wallafa wasu bayanan sirri da ya sama ta hanyar da ba ta dace ba.

Jaridar Le Courrier ta wallafa wani labari ne da ya shafi takaddama a gaban kotu tsakanin gwamnatin Nijar da kuma wani kamfani na kasar Lebanon, lamarin da ya sa jami’an tsaro suka cafke Ali Soumana, wanda shi ne dan jarida na baya-bayan nan da aka kama baya ga wani mai suna Baba Alpah da ya share kusan watanni hudu tsare a gidan yari.

Jaridar Soumana dai na cikin jaridun da ke adawa da gwamnatin Mahamadou Issoufou. A bara an taba tsare Soumana na tsawon kwanaki 10 bayan wallafa wani labari da ya shafi jami’an gwamnati.

Dokar Nijar ta 2010, ta haramta kame Dan Jarida inda ta bukaci ya biya kudaden tara akan laifukan da suka shafi keta aikin jarida a kasar.