rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Nijar UNICEF Wasanni

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Alfaga na Nijar ya zama jekadan UNICEF

media
Dan Nijar Issoufou Alfaga Abdoulrazak zakaran Taekwondo na duniya BOUREIMA HAMA / AFP

Hukumar UNICEF da ke kula da ilimin yara kanana ta Majalisar Dinkin Duniya ta nada Abdoulrazak Issoufou Alfaga, zakaran duniya na Taekwando dan kasar Nijar a matsayin jekadanta na musamman.


Alfaga ya kasance mutum na farko a Nijar da ya zama jekadan UNICEF, kuma zai shafe shekaru biyu yana aiki da hukumar.

A makon da ya gabat ne Alfaga ya lashe gasar Taekwando ta duniya da aka gudanar a Koriya ta kudu.

Dan wasan ya samu kyakkawar tarba bayan ya isa Nijar inda shugaban kasa Mahamadou Issoufou ya karrama shi da lambar yabo mafi girma a kasar.