Isa ga babban shafi
Najeriya

Ambaliyar ruwa ta yi barna a Kaita Jihar Katsina

Akalla mutane  2,000 sun rasa matsuguninsu a karamar hukumar Kaita da ke Jihar Katsina a Najeriya, sakamakon ambaliyar ruwar da aka samu da ta rusa gidaje sama da 150.

Za a fuskanci ambaliya a jihohin Najeriya
Za a fuskanci ambaliya a jihohin Najeriya RFIHAUSA/Awwal
Talla

Hajiya Umma Abdullahi Mahuta, kantomar karamar hukumar Kaita ta shaidawa RFI Hausa cewa ambaliyar ta janyo hasarar dukiyoya ta miliyoyin kudi.

Hajiya Umma ta ce ambaliyar ta fi barna a Unguwar Wakilin Kudu inda gidaje 69 suka rushe da kuma unguwar Wakilin arewa da yamma da sabuwar Unguwa duk a cikin garin na Kaita inda gidaje da shaguna da dama suka rushe.

Sai dai Hajiya ta ce ambaliyar ba ta janyo hasarar rai ba.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da Mukaddashin shugaban kasar Yemi Osibanjo ya bada umurnin sakin naira miliyan sama da dubu ga wasu Jihohin kasar domin taimakawa wadanda ambaliyar ta shafa.

A cikin makon nan gwamnatin Tarayyar ta yi gargadin cewa za a samu ambaliyar ruwa a jihohi 30 da kuma kananan hukumomi 100 da ke sassan kasar, sakamakon ruwan sama da ake tafkawa a daminar bana.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.