Isa ga babban shafi
Gambia

Gambia ta kafa kwamitin da zai binciki kadarorin Jammeh

Shugaban kasar Gambia Adama Barrow ya kafa wani kwamiti na musamman, da ya dorawa alhakin bincikar yadda tsohon shugaban kasar Yahya jammeh ya tafiyar da gwamnatinsa, da kuma kadarorin da ya mallaka.

Tsohon shugaban kasar Gambia Yahya Jammeh, a lokacin da yake barin kasar zuwa Equatorial Guinea, bayan kayen da ya sha a zaben shugabancin kasar na watan Disambar shekara ta 2016, a hannun Adama Barrow.
Tsohon shugaban kasar Gambia Yahya Jammeh, a lokacin da yake barin kasar zuwa Equatorial Guinea, bayan kayen da ya sha a zaben shugabancin kasar na watan Disambar shekara ta 2016, a hannun Adama Barrow. STRINGER / AFP
Talla

Kwamitin, zai binciki fannonin da suka hada da kwangilolin da gwamnatin Jammeh ta aiwatar, yadda gwamnatin ta sarrafa kudaden kasar, kadarorin da ya mallaka da kuma wadanda iyalai da mukarrbansa suka mallaka yayin zamanin gwamnatin ta Jammeh.

A watan Mayun da ya gabata gwamnatin Adama Barrow ta kwace kadarorin Yahya Jammeh, da aka kiyasta cewar darajarsu zata kai akalla dala miliyan 50, tare da rufe asusun ajiyar bankuna tamanin da ke da alaka da tsohon shugaban kasar.

A halin yanzu Jammeh yana gudun hijira a kasar Equatorial Guinea, sakamakon kayen da ya sha a zaben watan Disambar bara, bayan shafe shekaru 22 da biyu yana mulkin Gambia.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.