rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Rwanda Burundi

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Zaben shugabancin kasar Rwanda

media
Shugaban Rwanda, Paul Kagame, birnin Kigali, a ranar 2 ga watan agustan 2017. MARCO LONGARI / AFP

A ranar juma’a ake gudanar da zaben shugaban kasa a Rwanda inda Paul Kagame wanda ya shafe tsawon shekaru 17 kan karagar mulki ya sake tsayawa takara.


Shugaba Kagame ya taka rawa wajen inganta tattalin arzikin kasar, amma ana sukar lamirinsa saboda tsarinsa da wasu ke kallo a matsayin muzguna wa ‘yan adawa da kuma takaita fadin albarkacin baki.

A wannan alhamis ‘yan asalin kasar da ke zaune a waje sama da dubu 44 ne ke jafa nasu kuri’un domin zaben shugaba a wannan kasa da ta yi fama da rikicin kabilanci da ya yi sanadiyyar mutuwar sama da mutane dubu 800 a shekarar 1994.