Isa ga babban shafi
Libya

Khalifa Haftar ya tura da dakarun kasar zuwa gabar ruwan Libya

Mashal Khalifa Haftar, hafsan sojin da ke rike da muhimman yankuna a kasar Libya, ya umurci dakarunsa da su hana wa jiragen ruwan kasashen ketare matsowa kusa da gabar ruwan kasar.

Bakin haure na sauya hanyar shiga Turai ta Libya
Bakin haure na sauya hanyar shiga Turai ta Libya Reuters/Stefano Rellandini
Talla

Mai magana da yawun Haftar Khalifa Obeidi, ya ce umurnin ya fara aiki ne daga jiya, lamarin da kuma ake ganin cewa ya yi hannun riga da wani umurnin da firaministan kasar mai samun goyon bayan MDD Fayez al-Sarraj ya dauka ne, wanda ya bukaci kasashen duniya su aike da jami’an tsaron ruwansu domin hana baki tashi daga gabar ruwan zuwa Turai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.