Isa ga babban shafi
Kenya

Yan adawar kenya sun yi watsi da sakamakon zabe

Sakamakon farko dake fitowa daga  kasar Kenya na nuna cewar shugaba Uhuru Kenyatta ke kan gaba da kashi 55, yayin da Raila Odinga ke da kashi 44 daga cikin kuri’u miliyan 11 da aka kirga.Hadin kan Jam’iyyun adawar kasar Kenya dake goyan bayan Raila Odinga sun ki amincewa da sakamakon farko wanda ya nuna cewar shugaba Uhuru Kenyatta ya kama hanyar rike kujerar shugabancin kasar.

Hukumar zaben kasar Kenya a lokacin da a ke tattara sakamakon zabe
Hukumar zaben kasar Kenya a lokacin da a ke tattara sakamakon zabe REUTERS/Baz Ratner
Talla

Dan takara Raila Odinga yace hukumar zabe bata bada takardun shaidar dake nuna cewar Kenyatta ne ke kan gaba ba da kuri’un da suka zarce nasa ba, inda yace sakamakon na tattare da kura kurai.

Odinga yace wannan ya sasu fargaba lokacin da aka bada sanarwar kisan gillar da aka yiwa Chris Msando, jami’in kula da sashen tattara sakamakon zaben ta hanyar komputa.

Rahotanni dai sun ce an gudanar da zaben cikin kwanciyar hankali a akasarin fadin kasar, kuma yanzu haka hankula sun koma kan hukumar zaben mai zaman kan ta domin bada sakamako.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.