rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Senegal

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Jam'iyyun adawa za su kauracewa zabe a Senegal

media
Jagoran adawa a Senegal kuma tsohon shugaban kasar Abdoulaye Wade Reuters

Gamayyar Jam’iyun adawa a Senegal sun sanar da matakin kauracewa dukkanin Zabukan kasar masu zuwa a nan gaba sakamakon zargin tafka magudi a zaben wakilan majalisar kasar da ya gudana a baya-bayan nan. Sakamakon Zaben wanda hukumar zabe ta fitar a Juma'ar data gabata ya nuna cewa Jam’iyya mai mulki ta Shugaba Macky Sall ta lashe kujeru 125 a zauren majalisar.


Gamayyar Jamiyyun adawa a Senegal karkashin jagorancin tsohon shugaban kasar Abdoulaye Wade da ya sha kayi kaye a zaben 2012 bayan nasarar shugaba mai ci Macky Sally ta sami kujeru 19 a zaben majalisar kasar , yayinda jamiyar wani tsohon Magajin garin birnin Dakar Khalifa Sall ta sami kujeru 7.

Mai Magana da yawun gamayyar jam'iyyun adawar ya sanar da cewa ko kadan babu abinda zai sa su sake shiga wani zaben kasar karkashin Gwamnatin yanzu.

Zaben kasar na shekarar 2012 ya fito da kimar kasar a idon duniya, la'akari da yadda aka mika mulki lami lafiya ga jam'iyyar da ta yi nasara bayan kammala zabe.

Sai dai kuma a yanzu haka sakamakon zaben watan jiya na wakilan majalisar kasar na neman bata sunan kasar da neman kawo rudani ganin yadda bangarori daban-daban ke ci gaba da nuna rashin amincewa da sahihancin sakamakon.