Isa ga babban shafi
Najeriya

Matsalar rashin aiki ya karu a Najeriya da Afirka ta Kudu

Girman matsalar rashin ayyukan yi a Najeriya na dada karuwa da sama da kashi 14, a yayin da Afrika ta kudu adadin ya zarce kashi 27 kamar yadda wani binciken IMF ya nuna.

Shugabar Hukumar IMF Christine Lagarde
Shugabar Hukumar IMF Christine Lagarde REUTERS/Hannibal Hanschke
Talla

Binciken ya ce kananan kasuwanci ba zai iya magance matsalar rashin ayyukan yi ba a Afrika.

IMF ta ce kasashen da ke kudu da sahara na cikin hatsarin shiga wani yanayi a kasa da shekaru 20 idan har tattalin arzikinsu ba zai iya samarwa dimbin matasa ayyukan yi ba.

IMF ta ce za a fi samun yawan masu zaman kashe wando a Afrika a shekara ta 2035 fiye da idan an hade na sauran kasashen duniya baki daya.

A cewar rahoton na IMF kananan kasuwanci kamar tallace-tallace saman titi da aikin lebaranci ba su da wani tasiri ga bunksar tattalin arziki domin babu wani haraji da ake biya.

IMF ta ce kasashen da kananan kasuwanci ke da girma suna shafar ci gaban tattalin arzikin kasar,

kuma kasashe irinsu Najeriya da Tanzania kananan kasuwancin na tsakanin kashi 50 zuwa 65 ga ma’aunin ci gaban tattalin arzikinsu

IMF ta yi kira ga kasashen su mayar da hankali ga bunkasa kananan kasuwancin da mutane suka fi raja’a akai zuwa manya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.