rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Najeriya Majalisar Dinkin Duniya BOKO HARAM

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Jami’an tsaron Najeriya sun abka wani sansanin ma’aikatan MDD a Maiduguri

media
Dakarun Najeriya a Maiduguri Photo: Stefan Heunis

Majalisar dinkin Duniya ta ce jami’an tsaron Najeriya sun abka wani sansanin ma’aikatanta da ke kula da ayyukan jin kai a Maiduguri inda suka gudanar da bincike ba tare da sun sanar da ita ba.


Jami’an tsaron sun shafe sa’o’I uku suna bincike a sansanin a Maiduguri inda wasu bayanai ke nuna cewa sun kaddamar da binciken ne kan labarin da aka yada cewa shugaban Boko Haram na buya a sansanin.

Samantha Newport ita ce jami’ar hulda da jama’a ta ofishin kula da ayyukan jin kai a Najeriya kuma ta yi muna Karin bayani.