rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Libya

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Haramci ga jiragen ruwan kungiyoyi, da shawagi a gabar ruwan Libya

media
Bakin-hauren da suka isa gabar ruwan Libya ©REUTERS/Stefano Rellandini

Rundunar sojin ruwan kasar Libiya, ta haramtawa duk wani jirgin ruwan kungiyoyin agaji jinkai, dake aikin ceton bakin haure a gabar ruwan kasar, ci gaba da shawagi, har sai ya nemi izini daga gwamnati.


Kakakin rundunar sojan ruwan kasar ta Libiya Ayoub Kassem a wata sanarwa ya nuna kokarin hukumomin wuccin gadi na gudanar da aikin bincike da ceto a yankin na kasar Libya da cewa ya kamata jiragen kungiyoyin aiki ceto sun bi tsari tare da neman izini daga gwamnatin Libiya da kuma mutunta mahukumtan da abin ya shafa, da suka hada da masu tsaron gabar ruwa da kuma sojan ruwa.