rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Libya UNICEF Rikicin Kasar Libya

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

UNICEF ta ce yara rabin Miliyan ke bukatar taimako a Libya

media
UNICEF ta ce yara rabin Miliyan ke bukatar taimako a Libya Reuters//Max Rossi

Hukumar Kula da kananan yara ta Majalisar Dinkin Duniya, UNICEF, ta ce sama da yara rabin miliyan ke bukatar taimako a kasar Libya.


UNICEF ta bukaci bangarorin da ke ci gaba da gwabza fada a kasar da su yiwa Allah su sasanta tsakanin su.

Daraktan shiya na hukumar Geert Cappelaere y ace yara 550,000 ke bukatar taimako saboda yakin da ya raba su da matsugunin su, ya kuma haifar da matsalar tattalin arziki.

Hukumar ta ce kusan yara 200,000 basa samun tsaftacacen ruwan sha, yayin da 315,000 na bukatar taimako domin samun ilimi ganin yadda makarantu sama da 550 suka lalace sakamakon yakin ko kuma aka mayar da su matsugunin jama’a.