rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya Tarayyar Afrika

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Barazanar kungiyoyin tsageru a Afrika ta Tsakiya

media
Al'umar kasar Afrika ta Tsakiya Reuters

Wasu rahotanni daga Afrika ta Tsakiya na nuni cewa kasar na daf da sake fadawa cikin wani sabon rikicin kabilanci.


Rahoton da masana harakokin tsaro da zamantakewar dan Adam a karkashin hukumar Majalisar Dinkin Duniya suka gabatar na bayyana daya bayan daya ta yada wasu Shugabanin kabilu ke tattara matasa tareda basu makamai bisa korafin cewa wani bangaren alumar kasar ne ke morewa dinbin arzikin da kasar keda shi.

Afrika ta tsakiya mai yawan al’uma milyan hudu da dubu dari biyar ta fada cikin rikicin siyasa dama yaki basasa a shekara ta 2013.

Rikicin da ya hada musulman kasar da mabiya darikar katolikan na kasar.