rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Cote d'Ivoire

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Goyan bayan matasan Cote D'Ivoire ga Guillaume Soro

media
Guillaume Soro Shugaban Majalisar dokokin Cte D'Ivoire REUTERS/Thierry Gouegnon

Shugaban majalisar dokokin Cote D’Ivoire Guillaume Soro na ci gaba da samun goyan bayan wasu shugabanin matasa a kasar , goyan bayan dake zuwa a dai dai lokacin da wasu jam’iyun siyasar kasar ke cikin shiri domin sanar da dan takarar su a zaben shugabancin kasar na badi.


Soro wanda ya taba rike mukamin Firaminstan kasar ta Cote D’Ivoire kama daga shekara ta 2007 zuwa 2012 ba shi da jam’iyya, sai dai memba ne a jam’iyyar Shugaban kasar Alassane Dramane Ouattara.