rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Masar Sufuri

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Mutane 41 sun mutu a hatsarin jirgin kasa a Masar

media
Jiragen kasa biyu da suka yi taho-mu-gama a Masar KHALED DESOUKI / AFP

Alkalumman mutanen da suka rasa rayukansu a wani mummuan hatsarin jirgin kasa a Masar, sun haura zuwa 41.


A halin yanzu dai, jami’an agaji na ci gaba da amfani da kugiya don kwashe karafen jiragen biyu da suka yi taho-mu-gama a layin dogon da ke tsakanin biranen Al-Kahira da Askandariyya.

Hukumomin kasar sun cafke direbobin jiragen biyu don yi musu tambayoyi, yayin da kuma aka dakatar da jami’ai hudu da ke aikin kula da layin dogon har zuwa lokacin da za a kammala bincike kan aukuwar hatsarin.