Isa ga babban shafi
Somalia

Tsohon Jagoran Al Shabab ya mika wuya

Ma’aikatar tsaron kasar Somalia ta sanar da mika wuyan tsohon shugaban ‘yan-tawayen kasar Mukhtar Robow Abu Mansur bayan daya yanke alakar da ke  tsakaninsa da kungiyar Al Shabab. Dama dai tun a watan Yuli ne aka sanar da alaka tsakanin Robow da gwamnatin Somalia.

Rikici tsakanin kungiyar Alshabab da sojin gwamnati na ci gaba da lakume dubban rayukan fararen hular da basu ji ba basu gani ba
Rikici tsakanin kungiyar Alshabab da sojin gwamnati na ci gaba da lakume dubban rayukan fararen hular da basu ji ba basu gani ba Reuters/路透社
Talla

Tun a shekarar 2013 ne dai aka fara takun saka tsakanin Robow da kungiyar Al Shabab inda a lokuta da dama ta yi yunkurin halaka shi ko kuma kama shi ta hanyar kai mabambantan hare-hare kan maboyarsa, lamarin daya sa ya koma rayuwa a cikin dazuka tare da dakarunsa.

Tun bayan samun barakar ne kuma gwamnatin kasar ta aike da dakaru don bayar da kariya ga Robow lamarin da ake ganin ya kara tabbatar da yiwuwar mika wuyan Robow.

Duk da cewa dai akwai alaka mai karfi tsakanin Robow da gwamnatin kasar tun cikin watan Yunin daya gabata amma rahotanni sun ce ba a yi tsammanin mika wuyan tsohon jagoran cikin gaggawa ba.

A cewar wani babban Jami'in sojan Somalia Kanar Nur Muhammad yanzu haka Robow da dakarunsa bakwai na hannun hukumomi a kudu maso yammacin birnin Hudur inda kuma nan gaba kadan za a karasa da shi Magadishu babban birnin kasar.

Mika wuyan Robow dai na zuwa watanni biyu bayan Amurka ta janye batun bayar da ladar Dala miliyan biyar ga duk wanda ya yi nasarar kamashi.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.