Isa ga babban shafi
Kenya

'Yan adawa za su kauracewa aiki a Kenya

Jagoran 'yan adawa a Kenya daya sha kaye a zaben shugaban kasar Raila Odinga, ya yi ikirarin bayyana matakan gaba da zai dauka bayan zargin yi masa murdiya a zaben shugaban kasar da aka bayyana Uhuru Kenyatta a matsayin wanda ya lashe.

Magoya bayan Jagoran adawa Raila Odinga na ci gaba da nuna kin amincewarsu da nasarar shugaba Uhuru Kenyatta a zaben shugaban kasar
Magoya bayan Jagoran adawa Raila Odinga na ci gaba da nuna kin amincewarsu da nasarar shugaba Uhuru Kenyatta a zaben shugaban kasar Reuters
Talla

Odinga ya kuma bukaci magoya bayansa su kauracewa wuraren ayyukansu a ranar litinin don kalubalantar gwamnatin kasar kan zargin kitsa yadda zaben kasar zai kasance da kuma kashe ‘yan-adawa.

Da yake jawabi ga dandazon magoya bayansa a Nairobi babban birnin kasar Odinga ya ce an halaka daruruwan masu adawa da Uhuru Kenyatta a fafutukar neman hakkinsu da suka fito yi, a don haka dole a kauracewa a Gwamnatin.

Wannan dai shi ne karon farko da Raila Odinga ya fito ya yi jawabi ga taron magoya bayansa tun bayyana bayyana shi a matsayin wanda ya sha kaye a zaben.

Matakin dai na zuwa ne a dai-dai lokacin da zanga-zangar kin jinin shugaba Uhuru Kenyatta ke ci gaba da yin kamari a yammacin kasar dama wasu sassa na birnin Nairobi ciki har da Kibera da kuma Mathare lamarin da ya yi sanadin mutuwar kimanin 16.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.