Isa ga babban shafi
sierra-leone

Mutane 600 sun bace a ambaliyar Saliyo

Akalla mutane 600 sun bace bayan zabtarewar laka da ambaliyar ruwa da suka afka wa wasu yankuna na babbab birnin Freetown da ke Saliyo.

Ana ci gaba da neman mutane 600 da suka bace a ambaliyar ruwa a Saliyo
Ana ci gaba da neman mutane 600 da suka bace a ambaliyar ruwa a Saliyo REUTERS/Ernest Henry
Talla

An dai tabbatar da mutuwar mutane kusan 400 bayan aukuwar ibtila’in a farkon wannan makon.

A yau Laraban ne ake saran gudanar da jana'izar wasu mutanen da suka rasa rayukansu, matakin da zai rage cinkoson gawarwakin da aka jibge a dakunan ajiye gawarwaki.

Tuni shugaban kasar Ernest Bai Koroma ya bukaci taimakon gaggawa daga kasashen duniya, in da ya ce, ambaliyar ta share wuraren zaman al’umma.

Shugaban ya kuma bukaci jama’a da su kaurace wa yankunan da ibtila’in ya auku.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.