Isa ga babban shafi
kenya

Zan daukaka kara a kotun koli- Odinga

Jagoran ‘yan adawar Kenya Raila Odinga ya bayyana shirinsa na daukaka kara a kotun koli don kalubalantar sakamakon zaben shugabancin kasar.

Raïla Oding, jagoran 'yan adawar Kenya
Raïla Oding, jagoran 'yan adawar Kenya REUTERS/Siegfried Modola
Talla

Wannan na zuwa ne bayan Odinga ya zargi cewa, an tafka makudi a zaben, wanda shugaba mai ci Uhuru Kenyatta ya lashe.

Da farko dai, Odinga ya yi watsi da batun daukaka kara a kotu duk da cewa, kasashen duniya sun ba shi shawara shigar da karar a maimakon tayar da zaune tsaye.

A yanzu dai, Odinga ya amince ya shigar da karar don kalubalantar nasarar da abokin hamayyarsa Uhuru Kenyatta ya samu a zaben na makon jiya.

Odinga ya ce, a yanzu, sun yanke shawarar shigar da kara a kotun koli, in da ya ce, zai gabatarwa duniya irin shugabancin da Kenyatta ya samu da taimakaon makudin na’ura.

Mr. Odinga ya kuma bukaci magoya bayansa da su gudanar da zanga-zangar lumana, in da ya ce, kundin tsarin mulkin kasar ya bada damar gudanar da zanga-zanga da kuma shiga yajin aiki don nuna adawa da wani mataki.

Odinga mai shekaru 72 ya ce, zasu bi hakkokinsu kuma za su shafe tsawon dare tare da kada ganguna don janyo hankulan duniya kan rashin adalcin da aka yi musu a zaben shugabancin kasar kamar yadda ya fadi a babban birnin Nairobi a yaua Laraba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.