Isa ga babban shafi

Firaministan Congo Brazzaville ya ajje aiki

FADAR Shugaban kasar Congo Brazzaville ta ce Firaministan kasar Clement Mouamba tare da daukacin ministocin gwamnati sun ajje mukaman su. Sanarwar ajje aikin dai tazo ne kwanaki bayan da shugaban kasar Dennis Sassou Nguesso ya bayyana shirinsa na kafa sabuwar gwamnati.

Shugaban kasar Congo Brazzaville Dennis Sassou Nguesso tare da dandazon magoya bayan sa.
Shugaban kasar Congo Brazzaville Dennis Sassou Nguesso tare da dandazon magoya bayan sa. Reuters
Talla

A cewar shugaba Dennis Sassou Nguesso kafa sabuwar gwamnatin za ta taimaka wajen magance kalubalen tattalin arzikin da kasar ke fuskanta a shekarun baya-bayan nan.

Kasar Congo Brazzaville na daya daga cikin kasashen da suka dogara da sayar da man fetur, kuma faduwar farashin man a kasuwar duniya ta shafi kudaden da kasar ke samu.

Ya zuwa yanzu dai ba’a sanar da lokacin da za’a nada sabuwar gwamnatin ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.