Isa ga babban shafi
Mali

ICC zata yanke hukunci kan biyan diyya a Timbuktu

A wannan alhamis ake saran kotun hukunta manyan laifufuka da ke birnin Hague ta bayyana hukunci kan biyan diyyar wuraren tarihin da aka lalata a Timbuktu da ke kasar Mali.

Ahmad al-Faqi al-Mahdi Jagoran rusa gidan tarihin Timbuktu da ke Mali
Ahmad al-Faqi al-Mahdi Jagoran rusa gidan tarihin Timbuktu da ke Mali REUTERS/Patrick Post/Pool
Talla

Tuni dai aka yankewa mutumin da ya jagoranci lalata wuraren tarihin Ahmad al-Faqi al-Mahdi hukuncin daurin shekaru 9 a gidan yari.

Ana yiwa garin Timbuktu lakabin birni mai shehunai 333, saboda manyan malaman da aka binne a garin.

Azbinawa suka kafa garin a karni na 12, kuma a karni na 15 da 16 garin ya shahara wajen koyar da addinin Islama, inda mutane suka dinga zuwa daga wurare masu nisan domin samun ilimi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.