Saliyo ta shiga zaman makoki
Kasar Saliyo ta fara zaman makoki na mako guda sakamakon bala’in da ya afkawa kasar wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane sama da 300.
Wallafawa ranar:
Shugaban kasar Ernest Bai Karoma ya ce za’a sauke tutocin kasar, yayin da ya bukaci taimakon kasashen duniya domin tallafawa wadanda hadarin ya ritsa da su.
Hukumomi sun ce ya zuwa yanzu yara 105 suka mutu, yayin da ake neman wasu mutane 600 da suka bata.
Kazalika wasu rahotanni na cewa gawawaki na rubewa.
Majalisar Dinkin Duniya ta ce tana nazarin irin agajin da zata aikewa mutane kasar.
Kasar Israila da Hukumar Samar da Abinci ta WFP sun aike da kayan abincin da suka hada da shinkafa da man girki da za’a rabawa mutane 7,500 na makwanni biyu.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu