Afrika ta Kudu ta bai wa Grace Mugabe kariyar Diflomasiya
Gwamnatin Kasar Afirka ta kudu tace ta baiwa Uwargidan shugaban Zimbabwe Robert Mugabe kariyar diflomasiya, domin kaucewa tuhumar da ake mata na lakadawa wata mata duka a Johannesburg.
Wallafawa ranar:
Ministar kula da harkokin waje na Africa ta Kudu, Maite Nkoana Mashabane, tace daukar matakin abin ne mai wuya amma babu yadda suka iya.
Tuni Grace Mugabe da maigidanta suka koma Zimbabwe bayan ya kammala halartar taron kasashen dake yankin kudancin Afirka.
Tun bayan lakadawa matar duka, tare da ji mata rauni Grace Mugabe ta fara wasan ‘yar buya da jami’an tsaro, inda ko a ranar Asabar din da ta gabata, taki halartar taron shugabannin a lokacin da aka fara shi.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu