Isa ga babban shafi
Angola

Angola na zaben sabon shugaban kasa

Larabar nan al’ummar Angola ke kada kuri’ar zaben sabon shugaban kasa, matakin da zai kawo karshen mulkin Jose Eduardo Dos Santos wanda ya shafe shekaru kusan 40 yana shugabanci a kasar. Duk da dai Dos Santos ya kauracewa tsayawa takara amma ana sa ran dan takarar Jam’iyyarsa ta MPLA zai lashe zaben.

Shugaban Angola Jose Eduardo Dos Santos
Shugaban Angola Jose Eduardo Dos Santos Reuters
Talla

Ana ganin zaben dai a matsayin wani makamin tabbatar da sauyi a Angola, bayan shugaba Dos Santos ya ki yin tazarce wanda ya shafe shekaru kusan 40 yana mulki a kasar.

Sai dai Mutanen Angola da kuma masu lura da siyasar kasar na ganin babu makwa Joao Lourenco Dan takarar jam’iyya mai mulki ta shugaba Dos Santos ne zai lashe zabenm.

Kodayake wasu na ganin matasa da ke son canji na iya ba jam’iyya mai mulki mamaki musamman ganin yadda matasan suka fito suna goyon bayan manyan jam’iyyun adawar adawar kasar gufa biyu.

Tuni dai ‘yan adawa da wasu ;yan rajin kare hakkin bil’adama suka bayyana shakku akan sakamakon zaben saboda yadda aka mika takardun zaben ga sarakunan gargajiya .

Tun samun ‘yancin Angola a 1975 daga Portugal Dos Santos ke shugabanci a Angola

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.